الأحاديث الأربعون الفلسطينية
تأليف: د. جهاد جميل العايش آل عَمْلة
الكتاب متوفر باللغة العربية
Hadisai Arba’in akan Palasɗinu
Fassara Muhammad Musa Sambo da Dr Umar Ahmad Ibrahim
Muraja’a Dr Ibrahim Modibbo Umar
Pusat Studi dan Dokumentasi Baitul Maqdis.
جميع حقوق الملكية الأدبية والفنية محفوظة لـ ## مركز بيت المقدس للدراسات التوثيقية قبرص - نيقوسيا
ويحظر طبع أو تصوير أو ترجمة أو إعادة تنضيد الكتاب كاملاً أو مجزءاً أو تسجيله على أشرطة كاسيت أو إدخاله على الحاسوب أو برمجته على اسطوانات ضوئية إلا بموافقة خطية من المركز.
ردمك: 978-99966-624-0-9 رقم الإيداع: 237 / 2010 مكاتب مركز بيت المقدس للدراسات التوثيقية: فلسطين، لبنان، مصر، اليمن
موقع المركز على الإنترنت: www.aqsaonline.org البريد الإلكتروني: [email protected]
Hak Cipta dan Kekayaan Intelektual ada pada Pusat Studi dan Dokumentasi Baitul Maqdis Cyprus-Nicosia
Hak Cipta dilindungi undang-undang. Dilarang memperbanyak, menerjemahkan dan mencetak ulang, menggunakan kembali ilustrasi sebagian maupun seluruh isi buku ini, atau merekamnya ke dalam kaset, atau mengubahnya ke dalam bentuk elektronik seperti CD, tanpa izin tertulis dari penerbit.
Edisi Pertama: 1432 H/2011 M ISBN: 978-999-66-624-09 Nomor Dokumen: 237/2010
ردمك: 978-99966-624-0-9 – رقم الإيداع: 237 / 2010
Kantor Pusat Studi dan Dokumentasi Baitul Maqdis
Palestina
Gaza - Alremal - Thunourein Tower - Floor 6 - Mobile: +97082861654 Roaming Mobile: +970597994688 - +970599606142
Palestina
Nablus - St. Najjah - Telefax: + 970599606142 - Post Box : 463
Libanon
Seida - Quds Round by Hjazy Center - 1 St. Floor - Office 26 Mobile: +9613566070 - Phone : + 9617754789
Mesir
Cairo-Nassir City - Ten Superb-phone: +20224724656- Mobile: + 20109396601 For Correspondence: Post Office of Ten Suburb - Post No. 11528 - Po. Box: 39
Yaman
Sanaa - Hedat Al Madania - Opposite International Bank-Sylani Building 3 rd Floor - Office No. 8 - Phone: + 9671410471
Website:www.aqsonline.org E-mail: [email protected] Rekening Cairo: Faisal Islamic Bank-Cairo Central Branch-Account No. 261382 Sana’a: International United Islamic Bank-Sana’a Central Branch- Account No.00-101-483541 Wakif Markaz Bait Al Maqdis 0103-201017-001 Al-Baraka Bank Lebanon-Saida Branch
Faharisa
Lamban Hadisi – ma’ana – Shafi
- Gabatarwan mai fassara .... 9 - Gabatarwa .... 10 1- Masallacin Baitil Maƙdis shi ne Alƙiblar musulmi ta farko .... 15 2- Masallacin Baitil Maƙdis shi ne Masallaci na Biyu a doron ƙasa .... 16 3- Falalar Yin Sallah a Masallacin Baitil Maƙdis .... 17 4- Na ukun Masallatan da ake ziyara zuwa garesu .... 19 5- Falalar yin i’itikafi a cikin masallacin Baitil Maƙdis .... 20 6- Halaccin yin bakacen Sallah a Baitil Maƙdis .... 21 7- Buraqa dabban Manzon Allah ne Daga Makkah zuwa Baitil Maƙdis .... 22 8- Mu’ujizar tafiyar Annabi Muhammad daga Makkah zuwa Baitil Maƙdis cikin dare. .... 23 9- Annabi Muhammad (SAW) ya zaɓi Fiɗira a Masallacin Baitil Maƙdis .... 25 10- Annabi Muhammad (SAW) Limamin Annabawa a daren Isra’i cikin masallacin Aƙsa .... 27 11- Masallacin aksa yana bayyana ga manzon Allah a makkah don ya siffantashi ga ƙuraishawa .... 29 12- Annabi Muhammad (S.A.W) Yana ƙiran Nasaran (kiristocin) Baitil Maƙdis zuwa Musulunci .... 30
Lamban Hadisi – ma’ana – Shafi
13- Masallacin Aƙsa Harabar Masu Tsoron Allah ne 14- Annabi Musa (A.S) yana roƙon Allah da ya ɗauki ransa a kusa da ƙasar Palasɗinu 15- Riƙe rana a hana ta faɗuwa ga Yusha’u ɗan Nun 16- Annabi Sulaiman(A.S) ya sabanta ginin Masallacin Aƙsa 17- Tsaka tana ruruta wutar masallacin Qudus yayinda ya kone, Jemagu kuma suna kashe wutan 18- An ɗauki gawan Annabi Yusuf(A.S) zuwa ƙasa mai Albarka 19- Masallacin Aƙsa Mimbari ne na Annabawa 20- Annoban ƙasar Sham Shahada ne ga al’ummar Annabi Muhammad (SAW) sannan azaba ce ga kafirai. 21- Ginshiƙin Addini yana cikin ƙasar Sham 22- Annabi Muhammad (SAW) Yana yi wa sham Addu’ar Albarka 23- Falalar Hijra Izuwa ƙasar Sham 24- Tushen gidan muminai yana ƙasar Sham 25- Sham ita ce Maɓuyar muminai a ƙarshen zamani 26- Sham ita ce makomar jama’a masu cin nasara 27- Allah Ya lamuncewa ƙasar Sham da Mutanenta 28- Mala’ikun Allah sun shimfiɗa fukafukansu a kan ƙasar Sham 29- Idan Mutanen ƙasar Sham suka gurɓace to alkhairi zai tafi daga gareku
(Shafi, kamar yadda aka buga su a ginshiƙin: 32، 35، 37، 38، 40، 59، 61، 62، 64، 66، 67، 69، 70، 71)
Lamban Hadisi – ma’ana – Shafi
30- Asƙalan shi yafi falala wajen haɗe kawuna (dunƙulewa) a tafarkin Allah 31- Zuwan Khalifanci Baytul-Maqdis a ƙarshen zamani 32- Buɗe Baytul-Maqdis yana daga cikin alamomin tashin ƙiyama 33- Yawaitar ziyartar Baytil Maƙdis yana daga cikin alamar ƙarshen zamani 34- Dujjal ba zai shiga Masallacin Baitil Maƙdis ba 35- Yajuju da Majuju zasu shanye ruwan tafkin Ɗabriyya a ƙasar palasɗin 36- Dujjal yayi tambaya game da dabinan garin Baisan da tafkin Ɗabriyya a Palasɗinu 37- Annabi Isah zai kashe Dujjal a palasɗin 38- Annabi Isa (A S) Zai jagoranci mutane a Masallacin Maqdis 39- Bishiyoyi da duwatsu za su Tozarta Yahudawa a Palasɗinu 40- A sham za a tayarda matattu daga cikin kabari, kuma a ƙasar za a yi hisabi
(Shafi, kamar yadda aka buga su a ginshiƙin: 72، 74، 76، 78، 80، 81، 84، 86، 90، 93، 95، 97)
بسم الله الرحمن الرحيم
Bismillahir Rahmanir Rahim
Gabatarwan Mai Fassara
Godiya suƙara tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bamu ikon fassara wannan littafin mai suna “Hadisai guda Arba’in a kan Palasɗinu”.Sa’annan salati ga manzon tsira Annabi Muhammad (SAW) wanda aka turoshi ya zama shiriya ga halittu gaba ɗaya. Dalilin fassara wannan littafin kuwa shine sabida muhimmancin ƙasar Palasɗinu, domin tana daga cikin wurare na gurabun tarihi na addinin Musulunci, wanda a yanzu take ƙarƙashin mamayar Isra’ila. Sabida haka ya kamata duk Musulmi ya san muhimmancin wannan ƙasa ta hanyan sanin abinda ya faru a wurin da kuma abin da yake faruwa da kuma abinda zai faru nan gaba a nan ƙasar, wanda manzon tsira Annabi Muhammad (SAW) ya bamu labarinsa. Sai kuma godiya ga wa’enda suka ɗauki nauyin buga littafin.Da godiya ta musamman ga Dr. Ibrahim Modibbo Umar wanda yaɗauki nauyin karanta littafin da kuma gyara kura kurai na fassaran. Daga ƙarshe, in akwai gyara ko ƙarin bayani ko tambaya akan wannan fassaran sai ka tuntuɓemu a : [email protected]
Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata ga Annabinmu Muhammad, da iyalan gidansa, da Sahabbansa baki ɗaya. Bayan haka: Wannan matani ne a taƙaice wanda ta hanyarsa muke nufin farfaɗowa da raya sha’anin Palasɗinu, ƙasa mai tsarki a zuqatan mutane. Kuma mu ƙarfafa aƙidar miƙa wilaya ga wannan ƙasa tsarkakakkiya, kuma mu daɗa bayyana darajarta, da falalar masallacinta na ƙudus tare da dakarun kare su, kuma mu bayyana abubuwan da za su faru dashi har zuwa ƙarshen Duniya. Ta hanyar watsa Hadisan da suka inganta game da haka. Kuma mun zaɓo su ne ta hanyar tantancewa da kula, kuma ba tare da maimaitawan da zai sa a ƙosa ba. “Alhadisul Arba’un Al-Filisɗiniyyah” wato Hadisai guda Arba’in (40) da ke
magana a kan ƙasar Palasɗinu. Saƙo ne daga Annabin Allah (swt) da yake bayyana dangantakar tsarkakakkiyar ƙasar Palasɗinu da wannan Addini na Musulunci tun daga farkon zamani, tsakiyarsa da ƙarshensa.
Wannan littafi na Hadisi babi ne guda na ilimi da ake karantar dashi a masallatai da makarantu da zaurukan ilimi. A matsayin tsari na ilimi. Don tarbiyyantarwa da tabbatar da aƙida ingantacciya. zai dace ga Malamai da waɗanda suka goge a kan Da’awah su rungumi littafin wajen darussansu da wa’a’zozinsu, musamman a wannan zamanin da muryoyin ‘yan fafutuka da neman ‘yancin musulmin Palasɗinu da aka tauye, suka fara dushewa. Kuma ƙasar ta wayi gari a ƙarƙashin babakeren yahudawa marasa mutunci, marasa tausayi.
Tafarkin da muka bi wajen haɗa wannan
juzu’i na littafi na Hadisi shi ne, tafarkin ilimi da muka gada daga manyan magabatan malumanmu da manyan malaman Hadisai da suka gabata waɗanda suka yi rubutu a kan Hadisai ’yan arba’in’.
Bisa la’aƙari da irin wannan namijin ƙoƙari nasu ne tunanin samar da wannan littafi na Hadisai Arba’in a kan Palasɗinu ya taso. Mai yiwuwa, wasu su yi tambaya suce; To ai mafi yawan Hadisan sun zo ne da sunan SHAM amma to a nan zai yi kyau a yi tsokaci da cewa ita Palasɗinu yanki ne a wancan zamanin daga yankunan Sham kafin turawa su gutsuttsura ta, kamar yadda Shehin Malamin Tauhidin nan Yaqut Al-Hamani ya faɗa a cikin kundin littafinsa na tarihin Garuruwa da Birane juzu’i na 3 shafi na 321. Malamin ya zayyana iyakokin Palasɗinu kamar haka:
Girmanta ya fara daga kogin Furata zuwa
kurmin dake iyaka da ƙasar Misra, tsayinta kenan, faɗinta kuma daga Dutsen nan na Ɗaiyi dake kusurwar al-ƙibla ya nausa har zuwa gaɓar tekun Rum (wato Bahrur Rum). To ita kuma Palastinu yanzu tana gabashin Bahrul abyad ta gangaro ta yi iyaka da yammacin Asiya da kuma Arewacin Ifrikiyya.
A Taswirance kuma ta kasu gida huɗu ne, daga gabashinta har zuwa yammacinta.
Gaɓar Sahili (Kwazazzabai ne manya-
manya) Nabulus ƙudus da Khalilu (Kududdufan Urdun) Girmanta a yau ya kai kilomita Dubu Ashirin da shida da ɗari tara da casa’in (26990 Klm) wanda ya tattaro tekun Urdun daga gabas ta yamma kuma har zuwa Bahrul Abyad. Sannan ta yi iyaka da gaɓar kudancin Lebanon daga arewa kuma ta yi gaɓa da kogin Uƙbah daga kudu.
Dagaƙarshe ina miƙa godiyata ta
musamman ga ɗan’uwana Malam Nayif al-Farisi, saboda gudunmawar as h bayar wajen zaɓulo wasu Hadisan da aka yi amfani as h. Allah nake roƙo as h sanyawa wannan aiki karɓuwa a sararin ƙasan da ma samaniya kuma ya amfanar as hi a zantuka da aiyuka sannan ya rubuta mana ladansa har zuwa tsayuwar ƙiyama. Al-Hamdu Lillahi Rabbil- Alamin
Wanda ya tara hadisan Dan ƙasa tsarkakakkiya Jihad Jamil Al-Ayish
Hadisi Na Farko
### Masallacin Aƙsa Shi Ne Alƙiblar Musulmi Ta Farko
An karɓo daga Baban Ishaq, Allah Ya ƙara masu yarda ya ce: na ji Bara’u ɗan Azib yana cewa : “Mun yi sallah tare da Manzon Allah (SAW) kwatankwacin watanni goma sha-shida ko kuma shabakwai muka yi muna masu kallan Masallacin Aƙsa, sannan aka juyar da alqiblarmu zuwa ka’aba”(1).
1- Buhari ne ya ruwaito hadisin (6/27)(4492), da Muslim(1/374)(525) lafazin nashi ne, da Nasa'i(1/242) (475), da Ahmad(4/288)(18738).
Hadisi Na Biyu
### Masallacin Aƙsa Shi Ne Masallaci Na Biyu A Doron Ƙasa
An karɓo daga Abu Zarri yace :Nace : ya Manzon Allah wanne ne Masallaci na farko da aka gina a doron ƙasa(1) ?” Sai Manzon Allah ya ce “Masallacin Harami (Makkah)”, sai na ƙara cewa “Ya Kai Manzon Allah sannan wanne Masallaci?” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce : “sai Masallacin Al-aqsa(2) (Qudus)”, sai na ce
1- don yin Sallah a cikinsa.
2- an ambaceshi Al-aqsa ne sabida nisansa tsakaninshi da Ka'aba, Fathul-Bari(10/148).
Hadisi Na Uku
### Falalar Yin Sallah A Masallacin Aƙsa
An karɓo daga Abu Zarri ya ce : Mun yi tambaya a lokacin da muke a gaban Manzon Allah (SAW) a kan wannene ya fi falala, Masallacin Manzon Allah ko kuma Masallacin Aƙsa?” Sai Manzon Allah ya ce “Yin sallah sau ɗaya a wannan masallacin nawa ya fi falala a kan yin Sallah sau huɗu(1) a masallacin Aƙsa, madalla da wannan wurin sallah, lallai anyi kusa ya kasance mutum yana da gida
1- Annabi Muhammad(SAW) ya bada labarin cewa ladan yin Salla sau guda a cikin masallacin Manzon Allah na Madina dai dai yake da yin salloli dubu a waninsa; Manzon Alla(SAW) yace;"ladan yin Sallah a masallacina wannan ya fi ladan yin Sallah guda dubu a wani masallaci face Masallacin Harami(Ka'aba). buhari(1190), da Muslim(2/2012)(1394), da Tirmizi(2/147)(325), Nasa'i(5/214)(2899), da Ibn Maja(1/450)(1404).
misalin igiyan da yake daure dokinsa ta yanda zai iya hangan masallacin Aƙsa daga wannan gidan da yafi masa alheri da ya mallaki duniya da abinda yake cikinta”(1)
1-Ɗabarani ne ya ruwaito hadisin a cikin Al-Ausat(7/103)(6983), da Hakim(4/905).
Hadisi Na Huɗu
### Na Ukun Masallatan Da Ake Ziyara Zuwa Garesu
An karɓo daga Abu-Hurairah cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce : “Ba a ziyara sai zuwa ga masallatai guda uku, Masallacin Makka da Masallacin Manzo (Madinah) da Masallacin Aƙsa”(1)
1- Buhari ne ya rawaitoshi(4/491)(1189), da Muslim(2/1014)(1397), da Abu Dauda(2/216)(2033), da Nasa'i(2/37)(700), da Ibn Maja(1/452)(1409).
Hadisi Na Biyar
### Falalar Yin I’tikafi A Cikin Masallacin Aƙsa
An karɓo daga Huzaifah ɗan Yamani ya ce : lallai Manzon Allah (SAW) ya ce :“Ba a yin i’tikafi sai a cikin masallatai guda uku: Masallacin Makkah, da Masallacin Annabi, da Masallacin Aƙsa”(1).
1- Tahawi ne ya rawaitoshi a cikin"sharhin Mushkal"(1500),da Isma'ili cikin "Mu'ujam"(345) (2/112) da waninsu.
Hadisi Na Shida
### Halaccin Yin Bakacen Sallah A Baitil Maƙdis
Daga Jabir dan Abdullahi ya ce : lallai wani mutum ya tashi ranar Fatahu Makka sai ya ce ya Manzon Allah, lallai ni na yi bakace cewa in Allah ya baka galaba a kan Makkah to lallai zan yi sallah a Masallacin Baitil Maƙdis raka’a biyu, sai Manzon Allah ya ce “ka yi sallah a nan,” sai ya sake tambayar shi, sai “ya ce ka yi sallah a nan,” sai ya sake tambayar shi, sai ya ce “ka yi sallah a nan,” sai ya sake tambayar shi, sai ya ce da shi “to sha’aninka.”(1)
1- Abu Dauda ne ya rawaitoshi(2/255)(3305), da Baihaqi a cikin Sunan(10/82)(6026),da Ahmad(3/363) (14981) da waninsu.
Hadisi Na Bakwai
### Buraqa Dabban Manzon Allah Ne Daga Makkah Zuwa Baitil Maƙdis
Daga Anasɗan Maliki, lalle Manzon Allah(SAW) ya ce : an zo min da Buraƙa (shi dabba ne fariya fi jaki tsayi amma bai kai alfadari ba) yana ajiye ƙofatonsa a inda ganinsa ya tuƙe sai yace, sai na hau shi har na isa Baitil Maƙdis, sai na ɗaure shi a inda Annabawa suke ɗaure dawakansu, sannan sai na shiga Masallaci na yi sallah raka’a biyu sannan na fito, sai Mala’ika Jibril (Alaihis salam) ya zo min da wata ƙwarya ta giya da wata ƙwarya ta nono sai na zaɓi ta nono, sai Mala’ika Jibril ya ce: ka zaɓi fitira (sunnar Annabawa) sannan ya haura da mu zuwa sama(1).
1- Bukhari ne ya ruwaito (3887), da Muslim(1/162, 145)lafazin nashi ne, da Ahmad(6/216)(3499).
Hadisi Na Takwas
### Mu’ujizar Tafiyar Annabi Muhammad Daga Makkah Zuwa Baitil Maƙdis Cikin Dare
Daga Uwar muminai A’isha Allah ya ƙara masu yarda ta ce: “Lokacin da aka tafi da Annabi zuwa Masallacin ƙudus, sai mutane suka wayi gari suna ta maganganu a kan haka, wasu mutane suka yi ridda daga cikin waɗanda suka yi imani da shi suka gaskata shi suka tafi wajen Abubakar (R.A) da maganar. Suka ce: abokinka fa yana riyawar cewa an tafi dashi cikin dare zuwa Baitil maƙdis! Sai Abubakar ya ce: shin lallai ya faɗi haka? Sai suka ce : na’am. sai ya ce : in dai ya faɗi haka to haƙiƙa ya yi gaskiya. Sai suka ce: ka gaskata shi lallai cewa shi ya yi tafiya da daddare zuwa Baitil Maƙdis kuma har ya dawo kafin
asuba? Sai ya ce: na’am, lallai ni zan gaskata shi game da abin da ya fi nisan haka; zan gaskata shi da labarin sama da safe ko da daddare” saboda haka aka sami shi suna Abubakar mai gaskiya (ASSIDDIƙ)(1).
1- Imam Hakim ya ruwaito (3/62-63), kuma ya ingantashi,da Imam Azzahabi da Baihaqi cikin Dala'ilun Nububwwa(2/246)(652), Albani ya ingantashi cikin Silsilatus-Sahiha(306).
Hadisi Na Tara
### Annabi Muhammad(Saw) Ya Zaɓi Fiɗira A Masallacin Ƙudus
Daga Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce : “daren da aka yi tafiya da ni na ga Annabi Musa (A.S) sai gashi nan mutum ne mara jiki(siriri),mai tsefaffen gashin kai(tsabtatacce), kamar shi mutum ne wanda yake daga cikin mutanen garin Shanu’a(1). Sai na ga Isa (A.S) sai gashi nan mutum ne matsakaicin tsawo mai jar fata Kaman ya fito daga wurinwanka, kuma sai naga Annabi Ibrahim (A.S) ni nafiɗibar kamanni dashi cikin ‘ya’yansa. Sannan aka zo min da ƙore guda biyu, ɗaya ta giya ɗaya ta Nono, sai aka ce : sha wanda kake so, sai na ɗauki ta Nono na sha,
1- Shanu'a : unguwa ne a kasar Yaman sanannu ne wajen tsawo(dogayen mutane ne).
sai aka ce: kayi zaɓi na-gari, amma da ka ɗauki ta giya to da al’ummarka sun dilmiya(ɓata)(1).
1- Imam Bukhari ya rawaito shi(4/3394,186), kuma lafazin hadisin nashi ne, da Muslim(1/168/154), da Tirmizi(5/3130,300)kuma yace hadisi ne mai kyau kuma ingantacce, da Ahmad(2/281)(7776).
Hadisi Na Goma
### Annabi Muhammad (Saw) Limamin Annabawa A Daren Isra’i Cikin Masallacin Aƙsa
Daga Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah(SAW) ya ce : (Haƙiƙa na tsinci kaina ina cikin Hijiri Isma’il na kusa da Ka’abah ƙuraishawa na tambaya ta a kan tafiyata(Isra’i), sai suka tambaye ni a kan abubuwa daga Baitil Maƙdis wa’enda ban kula da su ba balle na iya tabbatar musu da su. Don haka sai na shiga ƙuncin da ban taɓa yin irin shi ba. Ya ce “sai Allah ya ɗago min masallacin ina ganinshi a gaba na, basu tambaye ni akan wani abu ba face na basu labarin sa,” kuma an nuna min ina cikin taron Annabawa, sai ga Annabi Musa a tsaye yana sallah sai gashi nan mutum ne mara
jiki(siriri)kamar shi mutum ne wanda yake daga cikin mutanen garin Shanu’a , sannan sai ga Annabi Isa ɗan Maryam (A.S) a tsaye yana sallah, wanda yafi kowa ɗibar kamanni da shi shi ne Urwatu ɗan Mas’ud Assaƙafi, can sai ga Ibrahim (A.S) yana tsaye yana sallah, wanda yafi kowa kamanni dashi shine abokinku, wato shi kansa Annabi Muhammad(SAW) kenan, sai lokacin sallah yayi sai ni na yi musu limanci. Bayan na idar da sallar sai na ji kira aka ce dani “ya kai Muhammad! Ga mala’ika mai gadin gidan wuta ka yi masa sallama, sai na waiwaya gare shi sai ya fara min sallama)(1).
1- Muslim ya rawaito shi(1/165)(172), da Ahmad(2/528)(10842), da Nasa'i(11220)(11416)
Hadisi Na Goma Sha Ɗaya
### Masallacin Aƙsa Yana Bayyana Ga Manzon Allah A Makkah Don Ya Siffantashi Ga Ƙuraishawa
Daga Jabir ɗan Abdullahi ya ce: “Lallai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Lokacin da ƙuraishawa suka ƙaryata ni(1) sai na tsaya a cikin ɗaki(2) sai Allah ya bayyana min Baitil Maƙdis(ina kallonsa) sai na fara basu labari game da ayoyinsa(alamominsa da yanayinsa) ina kallon sa(3).”
1- suka karyatani akan abin da na ambata masu na Isra'i suka nema da in faɗamasu alamomin Baitul Maƙdis.
2- daki: sunan garu ne da ya kewaye gefen dakin Ka'aba ta bangaren Sham (wato arewacin ɗakin Ka'aba) .
3- Bukhari(4710, 3886), da Muslim(1/156)(170), da Tirmizi(5/301)(3133), da Ahmad(3/377)(15099).
Hadisi Na Goma Sha Biyu
### Annabi Muhammad(S.A.W) Yana ƙiran Nasaran(Kiristocin) Baitil Maƙdis Zuwa Musulunci
Daga Zuhuri ya ce: Ubaidullahi ɗan Abdullahi ya bani labari, lallai ɗan Abbas, Allah ya ƙara musu yarda, ya bashi labari cewa, lallai Aba Sufiyanu ya bashi labari: “lallai Haraƙla ya aika masa da yaje alokacin suna Iliya’a(1), sannan sai ya kira da a kawo masa wasikar da Manzon Allah(SAW) ya turo,lokacin da ya gama karanta wasikar sai gurnani ya yawaita a wurinsa sai akayi ta ɗaga muryoyi da maganganu, sai aka fitar da mu daga wajen, sai nace ma abokai na lokacin da aka fitar damu : haƙiƙa lamarin dan Baban Kabsha(wato manzon
1- Iliya'a : Baitil Maƙdis.
Allah SAW) ya daukaka, lallai sarkin Banil Asfar( sarkin kasar Roma) yana tsoronsa(1).”
1- Bukhari ne ya rawaito(2978).
Hadisi Na Goma Sha Uku
### Masallacin Aƙsa Harabar Masu Tsoron Allah Ne
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud (R.A), daga Annabi (SAW) ya ce: “lallai Banu Isra’ila sun sanya khalifa bayan Annabi Musa (A.S), wata rana ya tashi yana sallah cikin dare a saman masallacin Qudus a farin wata sai ya tuna wasu al’amura da ya kasance ya aikatasu, sai ya fito sai ya sauko ta wani igiya wanda ya kasance yana rataye ne a cikin masallacin alhalin ya tafi, ya ce: sai ya tafi har sai da ya isa wurin wasu mutane da suke gaɓar rafi, sai ya same su suna buga bulok ko kuma suna yin bulok, sai ya tambayesu: Nawa kuke karɓa a kowani bulok ɗaya? Sai yace: sai suka ba shi labari, sai ya ci gaba da yin bulok tare da su. Sai ya zama ya na ci daga abin
da ya aikata da hannunsa(ma’ana yana cin guminsa) idan lokacin sallah yayi sai ya tashi yayi salla, sai ma’aikatan suka kai maganarsa zuwa wurin shugabansu cewa Lallai cikinmu akwai wani mutum yana yin kaza da kaza, sai sarkin ya tura da ya je, sai ya ƙi ya je, sau uku. Sai sarkin ya zo yana tafiya a kan taguwarsa, yayin da ya gan shi sai ya gudu shi kuma sai ya bi shi ya iske shi sai ya ce: “saurareni don nayi ma magana”, sai ya ce: sai ya tsaya har yayi Magana da shi, sai ya bashi labarinsa,da yaba shi labarin cewa da shi sarki ne amma ya gudu ya bar sarautar saboda tsoron Mahaliccinsa(Allah), sai yace “lallai ni ina da tabbacin zan bika,” “sai ya bi shi, sai suka bauta wa Allah su biyu, har sai da suka mutu a Rumailata(1) Misra.”
1- Sheikh Ahmad Shakir Allah ya yi masa Rahama Ya ce: ita "Rumaila" pili ce a karkashin ƙal'atul jabal, itace yanzu aka santa da suna Maidanu Salahud-din, kuma an santa da suna "Almunshiya" a Al-ƙahira.
Abdullahi ya ce : “da na kasance ina wurin da na nuna kabarinsu ta yadda Annabi ya siffanta mana(1).”
1- Albazzar ne ya rawaito(1990), da Ɗabarani(6599) (6/351), Albani yace hadisin sahihi ne(2833).
Hadisi Na Goma Sha Huɗu
### Annabi Musa (A.S) Yana Roƙon Allah Da Ya Ɗauki Ransa A Kusa Da Ƙasar Palasɗinu
Daga Abu Hurairah Allah shi kara yarda a gareshi ya ce: “An aiki mala’ikan mutuwa zuwa ga Annabi Musa, yayin da ya zo masa sai ya mare shi har sai da ya pasa masa idonsa, sai ya koma wurin Ubangijinsa sai ya ce: “Ka aike ni zuwa ga bawan da baya son mutuwa,” Sai ya ce: “Sai Allah ya mayar masa da idonsa,”Saiya ce: Ka koma wurin sa ka ce masa ya sanya hannunsa a kan bayan bijimi duk abinda hannunsa ya damƙa na gashin bijimin ga ko wani gashi ɗaya yana da shekara guda,Yace: Ya Ubangiji, sannan me zai faru? Yace: Sannan mutuwa. Sai Yace: a ɗauki rannawa yanzu sai Musa ya roƙi Allah da ya
kusantar dashi izuwa ƙasa mai tsarki ya kasance tsakaninshi da kasar kamar nisan jifa da dutse, Sai Manzon Allah(SAW) Ya ce: da ace na kasance a wurin da na nuna muku kabarinsa a gefen hanya a ƙarƙashin tararren yashi ja(1).
1- Bukhari(3407,1339), da Muslim(4/1842)(2372), da Nasa'i(4/118)(2089), lafazin na Muslim ne.
Hadisi Na Goma Sha Biyar
### Riƙe Rana A Hana Ta Faɗuwa Ga Yusha’u Ɗan Nun
Daga Abu Hurairah (R.A) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce”: “Ba’a taba tsare rana ga wani ɗan Adam ba sai dai a kan Yusha’u ɗan Nun daren da yayi tafiya zuwa Baitil Maƙdis(1).”
1- Ahmad ne ya rawaito(2/325)(829), da Khaɗib(9/99), da Ibn Asakir(21/229), Albani ya inganta hadisin(202) da (2226).
Hadisi Na Goma Sha Shida
### Annabi Sulaiman(A.S) Ya Sabanta Ginin Masallacin Aƙsa
Daga Abdullahi ɗan Amru ɗan As Allah ya yarda da su, daga Manzon Allah (SAW) “lallai Annabi sulaiman (A.S) ɗan Dauda yayin da ya gama gina masallacin Qudus sai ya roƙi Allah da ya ba shi hukuncin da zai yi dai dai da hukuncinSA, da mulkin da ba zai taɓa bawa wani bayansa ba, kuma duk mutumin da ya zo wannan masallacin babu wani abin da yake nufi sai dai ya yi sallah cikin masallacin face ya fitadaga kurakuransa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi(babu zunubi).” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Amma guda biyu an bashi su,” Manzon Allah (SAW) ya ce “ni ina fatan da ya kasance ambashi na
ukun(wato neman gafara ma duk wanda ya zo Masallacin)(1).”
1- Nasa'i(2/34)(693), da Ibn Majah(1/452)(1408), da Ahmad(2/176)(6644) da sauransu.
Hadisi Na Goma Sha Bakwai
### Tsaka Tana Ruruta Wutar Masallacin Qudus Yayinda Ya Kone, Jemagu Kuma Suna Kashe Wutan
Daga Qasim ɗan Muhammad, daga Aisha(R.A) lallai ita ta ce: “Tsaka ta kasance ranar da aka ƙona masallacin Qudus tana hura wutan da bakinta,Jemagu kuma suna kashe wutan da fukafukansu(1).”
1-Alfakihi ne ya rawaito shi a cikin littafinsa : Akhbaru Makka(3/398).
Hadisi Na Goma Sha Takwas
### An Ɗauki Gawan Annabi Yusuf (A.S) Zuwa Ƙasa Mai Albarka
Daga Abu Musa(R.A) ya ce “Wani balaraben ƙauye ya zo wajen Annabi (SAW) sai ya girmama shi,” sai ya ce: “Ka zo kusa mana” sai ya matsa sai ya ce: “Ka roƙi buƙatarka” sai ya ce: “Taguwa da zamu rinƙa hawa da kuma awakai da iyalaina suke tatsa.” Sai ya ce “shin kun gaza ne da ku zama kamar tsohuwar bani Isra’ila?” Sai Sahabbansa suka ce: “Ya Manzon Allah, mene ne labarin tsohuwar bani Isra’ila?” Ya ce “lallai Annabi Musa yayin da ya tafi da Bani Isra’ila zai fita daga Misra, sai hanya ta ɓace musu” sai ya ce: “Meye ke faruwa?” Sai Malamansu suka ce: “Mu ne ko zamu baka labara: lallai Annabi Yusuf yayin da mutuwa ta zo masa ya ɗauki alƙawari tsakaninmu da Allah
kada mu yarda mu bar Misra har sai mun ɗauki ƙasusuwan shi tare da mu.” Sai Annabi Musa Ya ce: “Waye ya san gurbin kabarinsa?” Suka ce: “babu wanda ya san inda kabarin Annabi Yusuf yake ba sai dai wata tsohuwa daga bani Isra’ila.” sai aka aika mata, sai ta zo, sai ya ce: “Ki nuna mun kabarin Annabi Yusuf.” sai ta ce: “a’a wallahi ni ba zan aikata ba har sai ka lamince min abu guda.” ya ce “Menene laminin naki?” Ta ce: “in kasance tare da kai a aljanna” sai ya ƙi ya bata wannan, sai Allah ya masa wahayi da ya lamunce mata, sai ta tafi da su izuwa wani ɗan ƙaramin rafi, wani wurin da ruwa ke taruwa (kwazazzabo) sai ta ce: “ku yashe wannan ruwan.” sai suka yashe. Ta ce “ku tona ku fito da ƙasusuwan Annabi Yusuf,” yayin da suka fito da shi tudu, sai ga hanya kamar hasken rana(1).
1- Abu Ya'ala(13/236)(7254), da Ibn Hibban(2/500) (723), da Hakim(2/439)(3523) kuma ya ingantashi.
Hadisi Na Goma Sha Tara
### Masallacin Aƙsa Mimbari Ne Na Annabawa
An karɓo daga Harisu ɗan Harisu Al-ash’ari, yardar Allah ta tabbata a gare su, lallai Manzon Allah(SAW) ya ce: “lallai Allah ya umarci Yahayaɗan Zakariyya da kalmomi guda biyar, da ya yi aiki da su kuma ya umurci Bani Isra’ila da su yi aiki da su.” Kai ka ce shi Yahaya ya yi jinkirin isar da wannan saƙo da Allah ya masa. Sai Allah ya yi wahayi ga Annabi Isah cewa: ko Annabi Yahaya ya isar da saƙon ko kai ka isar da shi. Sai Annabi Isa ya tafi gurin Annabi Yahaya, ya ce masa: lallai kai an umurce ka da kalmomi guda biyar da ka yi aiki da su, ka kuma umurci Bani Isra’ila su yi aiki da su, ko ka isar da wannan saƙo ko ni in isar. Sai ya ce masa(Annabi
Yahaya ya ce): Ya ruhin Allah, ni ina jin tsoron kar ka riga ni isar da wannan saƙo a sakamakon haka Allah ya yi mini azaba ko ya hallaka ni.” sai Annabi Yahaya ya tattaro Bani Isra’ila gaba ɗayansu a cikin Masallacin Baitil Maƙdishar sai da suka cika shi dam, sannan sai Yahaya ya hau ɗan wani tudu, sai ya gode wa Allah kuma ya yi yabo a gare shi sannan ya ce: “Lallai Allah ya umurce ni da kalmomi guda biyar nayi aiki da su. Kuma na umurce ku da ku yi aiki da su. Na farkon su shine : Ku bauta wa Allah kada ku tarai tashida wani, domin misalin wanda ya yi shirka da Allah, kamar misalin mutumin da ya sayi bawa da kuɗinsa ne, zinare ko azurfa, sannan ya zaunar da shi a cikin gida sai ya ce masa: ka yi aiki ka kawo min ladan aikin. Sai bawan ya ringa aiki yana kai ladan gurin wani mutum dabam banda mai gidansa, to wa ye
a cikin ku zai yarda da bawansa ya yi haka? Lallai Allah ya halicce ku, kuma ya azurtaku, ku bauta masa, kada ku yi shirka da shi da wani abu. Sannan ya umurce ku da kuyi sallah, idan za ku yi sallah kada ku yi waiwaye, saboda Allah yana fuskantar bawansa matuƙar bai waiwaya ba. Sannan ya umurce ku da yin Azumi, Misalin wanda ya yi azumi kamar misalin mutumin da a gurin shi akwai kwalbar turaren al-miski a cikin taron mutane masu yawa kowa yana jin ƙanshinalmiski, lallai warin bakin mai azumi shi ne mafi ƙamshi daga turaren al-miski a wurin Allah. Sannan ya umurce ku da yin sadaka, misalin wanda yake ba da sadaka kamar misalin mutumin da maƙiya suka kama shi sai suka ɗaure hannayensa zuwa wuyansa, sannan suka gabatar da shi don su sare wuyansa. Sai ya ce musu: shin zan iya fansar kaina daga gare ku? Sai ya
rinƙa fansar kansa da kuɗi kaɗan da kuma kuɗi mai yawa, har ya fanshi kansa. Sannan ya umurce ku da ku ambaceshi(zikiri) da yawa, misalin wannan wanda ya yi haka, kamar misalin mutumin da maƙiya suka bishi da gudu suna neman su kamashi sai ya zo wurin ɓuya sai ya ɓoye kansa a ciki. Lallai bawan Allahzai fi kare kansa daga shaiɗan idan yana ambatan Allah maɗaukaki. Lallai ni ina umurtanku da abubuwa guda biyar wanda Allah ya umurce ni da su:Ku lizimci jama’a, ku ji kuma ku yi ɗa’a (ɗa’a ma shugaba), da yin hijra, da yin jihadi saboda Allah, lallai duk wanda ya bar jama’a kwatankwacin taɓi haƙiƙa ya warware igiyar musulunci daga wuyansa, sai dai in ya dawo cikinsu. Duk wanda yayi ƙira irin ta jahiliyya to shi yana daga cikin wa’enda zasu gurfana a cikin wutar Jahannama, ko da yana azumi
kuma yana riyawar cewa shi musulmi ne. Ku yi ƙira irin ƙiran da Allah ya ambaceku da itawato musulmai, muminai bayin Allah ne(1).”
1- Tirmizi(2683), da Ahmad(4/130)(17302), Albani ya ingantashi(1724).
Hadisi Na Ashirin
### Annoban Ƙasar Sham Shahada Ne Ga Al’ummar Annabi Muhammad (Saw) Sannan Azaba Ce Ga Kafirai
An karɓo daga Baban Usaibu(R.A) badaɗen Manzon Allah (SAW) ya ce: Manzon Allah(SAW) ya ce: “Mala’ika Jibrilu ya zo min da zazzaɓi da kuma annoba, sai na karɓi zazzaɓi ga mutanen madina sai na aika da annoba zuwa ƙasar sham. Annoba shahada ce ga al-ummata kuma rahama ce gare su, sannan azaba ce ga kafirai(1).
1- Ahmad(5/81)(20786), kuma yana cikin Silsilatus-Sahiha(60)
Hadisi Na Ashirin Da Ɗaya
### Ginshiƙin Addini Yana cikin ƙasar Sham
An karɓo daga Abdullahi ɗan Amruwinɗan As Allah ya yarda da su ya ce: Manzon Allah(SAW) ya ce: “Lallai na ga ginshiƙin littafi (Qur’an) an cire shi daga ƙarƙashin matashi(pilo) na, sai na kalla saigashi nan haske ne mai yaɗuwa an tafi da shizuwa ƙasar sham. Ku saurara, lallai imani yana sham idan fitintinu suka afku(faru)(1).”
1- Ɗabarani(10/85), da Hakim(4/509)(8554).
Hadisi Na Ashirin Da Biyu
### Annabi Muhammad (Saw) Yana Yi Wa Sham Addu’ar Albarka
An karɓo daga ɗan Umar Allah ya yarda da su, ya ce: Annabi (SAW) ya ambata ya ce: “Ya Allah ka yi albarka a cikin sham ɗinmu, Ya Allah ka yi albarka a cikin Yaman ɗinmu.” Sai sahabbai suka ce: ya Manzon Allah har da ma Najduɗinmu! Sai ya ce: “Ya Allah ka yi albarka a cikin sham ɗinmu, Ya Allah ka yi albarka a cikin Yamanɗinmu” sai suka ce:ya Manzon Allah a cikin Najdu ɗinmu! Sai y ace, ina zaton cewa a na ukun ne yace: “game da Najdu a cikin ta za a yi girgizan ƙasa da kuma fitintinu, daga ita ne ƙahon shaiɗan zai ɓullo(1).”
1- Bukhari(7094), da Tirmizi(5/733)(3953), da Ahmad(2/118), da Ibn Hibban(16/290)(7301).
Hadisi Na Ashirin Da Uku
### Falalar Hijra Izuwa Ƙasar Sham
An karɓo daga Abdullahi ɗan Amruwinɗan As Allah ya yarda da su ya ce: na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Da sannu hijira za ta kasance bayan hijira, zaɓaɓɓun ma’abota ƙasa shine wanda ya fisu lizimtan wurin hijiran Annabi Ibrahim(wato Sham), sannan waɗanda za su rage sune ashararai a cikin ƙasa,ƙasar su zata ƙisu, Allah(SWT) zai ƙyama ce su, wuta kuma zata tarasu...tare da birrai da aladu.(1)”
1- Abu Dauda(3/4)(2482), da Ahmad(2/198)(6871), da Hakim(4/533)(8497).
Hadisi Na Ashirin Da Huɗu
### Tushen Gidan Muminai Yana ƙasar Sham
An karɓo daga Salamaɗan Nufail Al-kindi(R.A) ya ce: Manzon Allah(SAW) yace: “Tsakiyar/tushen gidan muminai yana Sham(1)”
1- Nasa'i(6/214)(3561), da Ahmad(4/104)(17006), da Hakim(4/494)(8383).
Hadisi Na Ashirin Da Biyar
### Sham Ita Ce Maɓuyar Muminai A Ƙarshen Zamani
An karɓo daga Salim ɗan Abdullahi ɗan Umar daga Babansa ya ce: Manzon Allah(SAW) ya ce:“Wata wuta zata bayyana a ƙarshen zamani daga “Hadramaut(1)” tana tara/koran mutane, sai muka ce: to me zaka umurce mu da mu aikata a wannan lokacin ya manzon Allah? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “na umurce ku da ku je ƙasar Sham(2)”
1- Hadramaut: gari ne kuma ƙabila ce a kudancin ƙasar Yaman.
2- Tirmizi(4/498)(2217) kuma ya ingantashi, da Ahmad(2/8)(4536), da Ibn Hibban(16/294)(7305).
Hadisi Na Ashirin Da Shida
### Sham Ita Ce Makomar Jama’a Masu Cin Nasara
An karɓo daga Sa’ad ɗan Abi-Waƙƙas (R.A) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mutanen yankin Sham ba za su gushe ba suna kan gaskiya har sai lokacin da za a yi tashin Alqiyama”(1).
1- Muslim(3/1525)(1925), da Bazzar(4/57).
Hadisi Na Ashirin Da Bakwai
### Allah Ya Lamuncewa Ƙasar Sham Da Mutanenta
An karɓo daga Wasila ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce:“Na umurce ku da Sham, saboda garin Sham shi ne mafi tsarki daga cikin garuruwan Allah waɗanda ya halitta, zaɓaɓɓun halittun Allah su suke zama a wannan wurin, amma duk wanda ya ƙi, to ya koma zuwa Yaman ɗinsa, ya ci gaba da sha daga kududdufansa(1), domin Allah ya lamunce min Sham da mutanenta.(2)”
1- Abin nufi shine, lizimtan kiwo da shayar da shuka ruwa.
2- Tabarani(22/58), Sahihut-Targib wat-Tarhib(3090).
Hadisi Na Ashirin Da Takwas
### Mala’ikun Allah Sun Shimfiɗa Fukafukansu A Kan Ƙasar Sham
An karɓo daga Zaidu ɗan Thabitu, ya ce: Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Madalla ga ƙasar Sham, sai Sahabbai suka ce: “Don me ya Manzon Allah?” Sai ya ce “Mala’ikun Allah ne suka shimfiɗa fukafukansu a kan ƙasar Sham”(1).
1- Tirmizi(5/734)(3954), da Ahmad(5/184)(21646), hadisin sahihi ne.
Hadisi Na Ashirin Da Tara
### Idan Mutanen Ƙasar Sham Suka Gurɓace To Alkhairi Zai Tafi Daga Gareku
An karɓo daga Mu’awiyya ɗan ƙurrah, ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan mutanen Sham suka gurɓace (daga bin tafarki na ƙwarai) to babu alkhairin da zai saura a cikinku,wasu Jama’a daga cikin al’ummata ba za su gushe ba Allah na taimakon su, wanda ya taɓar da su ba zai cutar da su ba har zuwa ranar alƙiyama”(1)
1- Tirmizi(4/485), da Ahmad(3/436)(15635), Sahihul-Jami'i(702).
Hadisi Na Talatin
### Asƙalan Shi Yafi Falala Wajen Haɗe Kawuna (Dunƙulewa) A Tafarkin Allah
An karɓo daga ɗan Abbas, Allah ya ƙara musu yarda (ɗan da Ubansa), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Farkon wannan al-amari annabtane da tausayawa(Rahama), sai Khalifanci da tausayawa ya biyo baya, sai mulki da tausayawa ya biyo bayansa, daga baya mutane za su yi riƙo dashi irin yanda jakuna suke cizo da haƙoran su, don haka ina horonku da yin jihadi, kuma mafificin jihadi a gareku shi ne Ribaɗi (wato tsare iyaka), kuma mafificin ribaɗi” to yana garin Asƙalani(1).
1- Tabarani(11/88)(11138), silsila sahiha(3270).
Hadisi Na Talatin Da Ɗaya
### Zuwan Khalifanci Baytul-Maqdis A Ƙarshen Zamani
An karɓo daga Abdullahi ɗan Hawalat Al-Azdi, yace: Manzon Allah (SAW) yace: “Ya kai ɗan Khawalat Idan ka ga Khalifanci ya sauƙa a ƙasa mai tsarki, to haƙiƙa girgizar ƙasa, da bala’i da manya manyan al-amurra ya kusa, kuma tashin ƙiyama a wannan lokaci ya fi kusa da mutane fiye da nisan da ke tsakanin hannuna da kanka(1)”
1- Abu Dauda(3/19)(2535), da Bukhari fit-Tarikh (8/436), da Sahihu Abi Dauda(2535).
Hadisi Na Talatin Da Biyu
### Buɗe Baytul-Maqdis Yana Daga Cikin Alamomin Tashin Ƙiyama
An karɓo daga Auf ɗan Malik, ya ce: “Na je gurin Manzon Allah (SAW) a yaƙin Tabuka, a lokacin yana cikin shema wacce aka yi ta daga fata, sai ya ce: “Ka ƙirga abubuwa guda shida wanda suke kusa da tashin alƙiyama: Mutuwata, sai buɗe Masallacin Qudus, sai yawan mace mace da za ta kama ku kamar yadda cutar ƙu’as(1) yake kama dabbobi, sannan yawaitar dukiya, wanda har in an ba mutum dinari ɗari sai ya ɗori yin fushi, sai wata fitina da zata kunno kai, wacce baza ta bar wani gida na balarabe ba face sai ta shiga, sa’annan sai huduna da zata kasance tsakaninku
1- cutar ƙu'as: cut ace dake kama dabbobi sai wani abu ya zubo ta hancin su, sai su mutu nan take.
da Romawa, sai su yaudareku sai su zo maku ta ƙarƙashin tutoci guda tamanin, a ƙarƙashin ko wace tuta akwai mutum dubu goma sha biyu”(1).
1- Bukhari(4/123)(3176), da Ibn Majah(2/1341)(4042).
Hadisi Na Talatin Da Uku
### Yawaitar Ziyartar Baytil Maƙdis Yana Daga Cikin Alamar Ƙarshen Zamani
An karɓo daga Mu’azu ɗan Jabal(R.A) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Yawaitar ziyartar Baytil Maqdis shine zai kasance dalilin rushewar Yathriba(Madina), dalilin rushewar Yathriba(Madina) kuma shine ɓullowan babban paɗa(yaƙi), idan babban paɗa ta ɓullo to bayan ta ne za’a buɗe ƙasar Qasɗanɗiniyya, idan aka buɗe ƙasar ƙusɗanɗiniyya kuma to sai fitowar Dujjal.(1)”
1- Abu Dauda(4/110)(4294), Sahihul-Jami'is-Sagir.
Hadisi Na Talatin Da Huɗu
### Dujjal Ba Zai Shiga Masallacin Ƙudus Ba
An karɓo daga wani mutum daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) ya ce: Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Ina muku gargaɗi daga fitinar Dujjal, domin babu wani Annabi da ya zo ya wuce face sai ya gargaɗi mutanensa ko kuma al-ummarsa daga fitinarsa (Dujjal). Shi mutum ne baƙi baƙi,mai murɗaɗɗen gashin kai,mai shafaffen ido ɗaya na hagu, zai saukar da ruwan sama amma ba zai iya fidda tsirrai ba, kuma za a ba shi ikon kashe rai, sai ya dawo da ran bayan ya kashe ta,ba za a ba shi iko a kan wanin ran ba, kuma zai zo da aljanna da wuta, da ruwa da korama da kuma dalar waina (Khubz), kuma lallai aljannarsa wuta ce, sannan wutarsa itace aljanna,
zai kasance tare da ku har tsawon kwana arba’in, zai shigako ina cikin duniya amma banda masallatai huɗu: Masallacin Makka mai alfarma da Masallacin Madina da Dutsen ɗur da kuma Masallacin Baitil Maƙdis. Idan ya shige muku duhu ko yayi kama da wani, to ku sani lallai Allah Ubangijinku ba mai ido ɗaya bane.(1)”
1- Ahmad(5/434)(23734), silsiltus-Sahiha(2934).
Hadisi Na Talatin Da Biyar
### Yajuju Da Majuju Zasu Shanye Ruwan Tafkin Ɗabriyya A Ƙasar Palasɗin
An karɓo daga Al-Nawwas ɗan Sam’an daga Annabi (SAW) ya ce: “Sannan Allah zai tayar da Yajuju da Majuju, za su rinƙa sauri a cikin dukkan kwazazzabun ƙasa, na farkonsu za su taho tafkin Ɗabriyya, sai su shanye ruwansa, na ƙarshen su sai su zo gurin, sai su ce: “ai da akwai ruwa a nan” Sai su wuce ba za su tsaya ba sai sun isa dutsen Khamar, shi wani dutse ne da ke Baitul Maqdis, sai su ce: “Haƙiƙa mun kashe waɗanda ke doron ƙasa, ku zo mu kashe waɗanda suke sama,” sai su harba masun su zuwa sama, sai Allah ya maido musu da masunsu a shafe da jini”(1).
1- Muslim(4/2250)(2937), da Tirmizi(4/510)(2240).
Hadisi Na Talatin Da Shida
### Dujjal Yayi Tambaya Game Da Dabinan Garin Baisan Da Tafkin Ɗabriyya A Palasɗinu
An karɓo daga Fatima ‘yar ƙays, Allah ya ƙara mata yarda ta ce:Lallai Annabin Allah ya hau mimbari wata rana sai ya yi dariya, ya ce: “lallai Tamimu Addari ya bani wani labari, sai ya faranta min rai, shi ne nake son in baku labarin: “ya bani labari cewa, lallai wasu mutane daga mutanenpalasɗin sun hau jirgin ruwa suna tafiya a cikin kogi, sai igiyar ruwa ta ɗibe su har sai da ta kai su wani tsibiri daga cikin tsibiran kogin, sai suka haɗu da wata dabba gashinta a hargitse, sai suka ce: ke wacece? Sai tace: Ni mai leƙen asiri ce, sai suka ce: ki bamu labari, sai tace: bazan baku labari ba, kuma ba zan nemi labarinku ba, sai dai kuje can ƙarshen
gari, a can za ku samu wanda zai baku labari kuma ya nemi labari daga gurinku, sai muka je ƙarshen garin, sai ga wani mutum an ɗaure shi da sarƙa, sai yace mana: ku bani labari game da Koramar Zugar, Sai muka ce masa: tana nan tana ambaliyar ruwa, sai ya ce: mene ne game da tafkin(Ɗabriyya )? Muka ce masa: Itama tana ambaliyar ruwa, sai ya ce: ku bani labarin Dabinan Baisan wanda yake tsakanin ƙasar Urdun da Falasɗin,shin yayi’ya’ya kuwa ? sai muka ce: E. sai yace: To ku bani labarin Annabi, shin an aiko shi? Sai muka ce: E. sai ya sake cewa: ku bani labari yaya mutane suka riƙe shi? Sai muka ce; suna gaggawan karɓar kiransa , sai yace: sai ya zabura zabura, sai muka ce; kai wane ne? sai ya ce: Ni Dujjal ne, sai Manzon Allah ya ce: “Zai shiga duk wani gari ban da Ɗaiba, Ɗaiba itace Madinah”(1).
1- Muslim(4/2261)(2942), da Abu Dauda(4326), da Tirmizi(4/521)(2253) da Ahmad.
Hadisi Na Talatin Da Bakwai
### Annabi Isah Zai Kashe Dujjal A Falasɗin
An karɓo daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya shiga guri na a lokacin ina kuka, sai ya ce min: me ya saki kuka? Sai na ce: Ya manzon Allah! Na tuno da (al’amarin) Dujjal ne, shi ne nake kuka.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “In Dujjal ya fito a lokacin ina raye, to na isar muku daga sharrinsa, idan kuma ya fito bayan bana nan, to ku sani lallai Ubangijinku ba mai ido ɗaya ba ne, kuma shi Dujjal zai fito ne daga cikin Yahudawan garin Asbahan(1), har ya iso Madina, sai ya zo ga ganuwarta, a wannan
1- Asbahan: gari ne a ƙasar Iran tana nesa da Tehran ta arewa gwargwadon nisan kilomita 340, Musulunci ya shigeta a lokacin Khalifancin Sayyidina Umar(R.A).
lokacin tana da ƙofofi bakwai ne, a kowace ƙofa akwai Mala’iku biyu, sai ashararanta (Madinah) su fito zuwa gare shi, (zai kasance a duniya yana zagawa) har sai ya zo ƙofar garin Luddu(1) a ƙasar Falasɗin, sai Annabi Isa ya sauƙo(daga sama), ya kashe shi. Annabi Isa zai kasance a duniya bayan kashe Dujjal tsawon shekara arba’in, yana matsayin shugaba mai adalci, kuma mai hukunci da adalci”.(2)
1- Luddu: gari ne a ƙasar Palasɗinu.
2- Imam Ahmad ne ya rawaito (6/75)(24511), da Ibn Hibban(15/235)(6822).
Hadisi Na Talatin Da Takwas
### Annabi Isa Zai Jagoranci Mutane A Masallacin Maqdis
An karɓo daga Abu Hurairah, Allah ya ƙara masa yarda ya ce: Na ji Baban Al-ƙasim mai gaskiya kuma abin gasƙatawa yana cewa: “Lallai Dujjal mai ido ɗaya …..zai fito ta ɓangaren gabas, a lokacin da mutane suka rarrabu kuma suke cikin saɓani, zai zagaya ƙasa iya abin da Allah ya so da ya zagaya a cikin kwana arba’in, Allah ne kawai ya san kwatankwacin inda zai zagaya, kuma muminai za su shiga cikin tsanani mai yawa, daga nan sai Annabi Isaɗan Maryam ya sauko daga sama, sai ya jagoranci mutane a Sallah, idan ya ɗago kansa daga ruku’insa sai ya ce: Sami’allahu Liman Hamidah, Allah ya kashe Dujjal mai shafaffen ido, kuma ya baiwaMusulmai nasara”.(1)
1- Ibn Hibban(15/223)(6812).
Hadisi Na Talatin Da Tara
### Bishiyoyi Da Duwatsu Za Su Tozarta Yahudawa A Palasɗinu
An karɓo daga Abu Hurairah, lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi ya ce: “Ba za a yi tashin al-ƙiyama ba har sai musulmai sun yi yaƙi da Yahudawa , sai Musulmai su karkashe su, har sai bayahude ya ɓuya/fake a bayan dutse da itaciya, sai dutsen ko bishiyar ta ce: Ya kai Musulmi, ya kai bawan Allah!, ga wani bayahude a bayana ya ɓoye, zo ka kashe shi, sai dai wata itaciya mai suna “Garƙad(1)” domin tana daga cikin bishiyoyin Yahudawa.”(2)
1- Garƙad: wani nau'I ne na bishiya mai ƙaya.
2- Buhari(4/51)(2926), da Muslim(4/2239) kuma lafazin nashi ne, da Ahmad(2/417)(9387).
Hadisi Na Arba’in
### A Sham Za A Tayarda Matattu Daga Cikin Kabari, Kuma A Ƙasar Za Ayi Hisabi
An karɓo daga Abu Zarri(R.A) ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: “A sham za a tayar da matattu daga cikin kaburbura kuma a ƙasar za ayi Hisabi.”(1)
1- Baihaƙi(3/486)(4145), da Ɗabarani(8/148)(8230).
ساهم معنا في ترجمة «الأربعون الفلسطينية» إلى اللغات العالمية
الإنجليزية * البوسنوية * الأندونيسية * الألمانية الإسبانية الإيطالية البرتغالية اليابانية الكورية الصينية الأوردية الفلبينية الهندية الأوكرانية الأيرلندية البلغارية الروسية اليونانية الهنغارية الفتنامية الكرواتية النيجيرية
* تم ترجمته وينتظر المساهمة في الطباعة تكلفة (٥٠٠٠) نسخة من كل إصدار بتكلفة (٢٠٠٠) دولار امريكي تقريباً.
اسحب الصفحة أو استعمل الأسهم للتقليب، وحدّد أي نص لنسخه مع إحالته.
للتصحيح: راسلنا مع رقم الصفحة.
